Mahukuntan Najeriya sun ce, an kammala dukkanin shirye shiryen da suka kamata, domin rufe filin tashi da saukar jiragen saman kasa da kasa dake birnin Abuja, fadar mulkin Najeriya.
Da yake tabbatar da hakan a jiya Litinin yayin wani taron manema labarai, karamin ministan sufurin sama a Najeriyar Hadi Sirika ya ce, za a rufe filin jirgin na Nnamdi Azikwe ne har tsawon makwanni 6, domin gudanar da gyare gyare ga titin saukar jiragen dake cikin sa.
Sirika ya ce tun da fari, an gina titin tashi da saukar jiragen ne bisa wa'adin aiki na shekaru 20, amma a yanzu haka an yi amfani da titin sama da shekaru 34 ba kuma tare da wani kyakkywan gyara ba.
Yayin da filin jirgin yake a rufe, gwamnatin Najeriyar ta ce za a yi amfani da filin jirgin sama na garin Kaduna dake arewa maso yammacin kasar, sa'an nan a rika amfani da motocin bas, da jiragen kasa, ko jirage masu saukar angulu wajen sufurin fasinjoji daga Kaduna zuwa birnin tarayya Abuja.
Ministan ya kuma kara da cewa, da yawa daga kamfanonin jiragen sama dake sufuri a cikin kasar, sun amince da sauyawa zuwa filin saman na Kaduna, yayin da suke ci gaba da kokarin gamsar da manyan kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa su amince da karkata zirga zirgar su zuwa Kaduna. Ya ce, gwamnati ta dauki kwararan matakai na tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin fasinjoji, da za su yi zirga zirga ta filin jirgin saman karin na Kaduna.(Saminu)