Wata kotu dake zaman ta a birnin Yola na jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, ta yankewa tsohon gwamnan jihar James Bala Ngilari, hukuncin zaman kaso na shekaru 5 ba tare da zabin tara ba.
Hukumar EFCC mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar zagon kasa ce dai ta gabatar da kara gaban kotun a watan Satumbar bara, bayan kuma nazartar shaidu, mai shari'a Nathan Musa na babbar kotun tarayya, ya tabbatar da cewa, an samu Ngilari da laifuka masu alaka da karya dokokin sayen kadororin gwamnati.
Shari'ar dai na da alaka ne da batun sayen wasu motocin gwamnati guda 25, kan kudi Naira miliyan 167 ba tare da bin tsarin da doka ta tanada ba. Mai shari'a Musa ya ce, shekaru 5 a gidan kaso, shi ne mafi sassaucin hukunci ga Ngilari. Kaza lika shari'ar wanda ya ce Ngilari na iya zabar kurkukun da zai shafe shekarun 5, ya kara da cewa, hukuncin wani darasi ne ga sauran jami'an gwamnati dake sha'awar karya dokokin kasa.
To sai dai jim kadan da yabbana hukuncin, lauyan tsohon gwamnan Samuel Toni, ya ce za su daukaka kara.(Saminu)