in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF: Sin na iya cimma burinta na bunkasar tattalin arziki
2017-03-10 09:43:48 cri

Asusun ba da lamuni na IMF, ya ce kasar Sin na iya cimma burin ta na samun karuwar GDP a kan kaso 6.5 bisa dari a bana, sai dai kuma akwai bukatar ta aiwatar da karin sauye sauye, wadanda za su dora tattalin arzikin na ta kan hanya mai dorewa.

Kakakin asusun na IMF Gerry Rice ne ya bayyana wa wakilin kamfanin dillancin labarai na Sin Xinhua hakan, yayin wani taron manema labarai. Mr. Rice ya ce, "Muna ci gaba da ba da shawarar rage burin bunkasar karuwar GDP kadai, tare da mai da hankali ga karuwar tanadi na basuka, da lura da bukatun kasafin kudi a sashen ayyukan hukuma, tare da kara raya zamantakewar al'ummar kasar".

Yayin gabatar da rahoton gwamnatin kasar Sin da ya gudana a ranar Lahadi, an bayyana cewa, kasar na fatan GDPn ta na bana zai samu karuwa zuwa kaso 6.5 bisa dari, adadin da ya gaza 6.5 zuwa 7 da ta samu a bara, daidai da hasashen da IMF din ya yi a watan Janairun da ya gabata.

Da yake karin haske game da hakan, tsohon jami'in babban bankin duniya Mr. David Dollar, ya ce hasashen matsakaicin karuwar GDP da kasar Sin ke yi, na nuna yadda gwamnatin kasar ta amince da burin samun ci gaba sannu a hankali, a wani mataki na ci gaba da yin tasiri cikin kasuwar cinikayya wadda ke tattare da hadurra.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China