in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya ce, bunkasar bankunan Afirka na tattare da kalubale
2015-02-06 10:55:37 cri

Wani sabon rahoton da asusun ba da lamuni na IMF ya fitar, ya ce, ci gaban da bankunan Afirka ke yi na da ma'anar gaske ga ci gaban nahiyar, sai dai a daya hannun hakan na tattare da wasu matsaloli.

Rahoton na IMF ya ce, batun tantance yadda wadannan manyan bankuna na Afirka ke gudanar da ayyukansu, na haifar da kalubale ga wasu kasashen nahiyar.

A cewar wancan rahoto, akwai bankunan Afirka dake da rassa 36 a kasashen nahiyar daban daban, wadanda suke da tasiri matuka fiye da takwarorin na Turai da Amurka dake cikin nahiyar. Kaza lika rahoton ya ce, a yanzu haka, akwai a kalla bankunan nahiyar 7, dake hada-hada a kasashen nahiyar 10, ciki hadda 3 dake da helkwata a Morocco, da 2 masu helkwata a kasar Togo, da kuma wasu daidai dake da babban ofishinsu a Najeriya da Afirka ta Kudu.

Sai dai duk da wannan ci gaba, babban kalubalen, a cewar IMF shi ne na sanya ido game da ayyukansu, da kuma karancin kudade da suke samarwa a kasashen nahiyar da dama. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China