in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IMF ya fitar da hasashe mara kyau a tattalin arzikin Afrika ta Kudu
2015-06-24 11:02:09 cri

Ci gaba da kuma samar da ayyukan yi a kasar Afrika ta Kudu har yanzu suna fuskantar mawuyancin hali, sai dai rashin karfin daga waje ya fara sassautawa, kamar yadda hasashen asusun ba da lamuni na duniya IMF ya nuna a ranar Talatan nan.

Hadarin da hauhawar ci gaban zai fuskanta a kasar ya hada da karancin wutar lantarki, matsalar huldar tsakanin gwamnatin kasar da ma'aikata, rikicin kasuwannin kudi na duniya, da tafiyar hawainiya a wannan fanni, in ji rahoton na IMF.

Hasashen da IMF din ya yi na hauhawar ci gaba a Afrika ta Kudun zuwa kashi 2% a shekarar 2015 da 2016, sake hadewa da kashi 2.8% a cikin matsakaicin lokaci, da kuma hasashen karuwan samun makamashin

Asusun IMF ya kuma yi hasashen cewa, bashin da ake bin kasar zai daidaita da kusan kashi 50% na ma'aunin GDP nan da shekara ta 2019 da ta 2020, wanda ya yi kasa da kashi 56% da aka riga aka yi hasashen shi a shekara ta 2014.

Ci gaba a bangaren ciniki ya dan sauke hauhawar kayayyakin masarufi, kuma ya rage rashin karfin shi daga waje, in ji IMF. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China