in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta fice daga ICC
2015-10-12 10:14:47 cri

A ranar Lahadi, jam'iyyar African National Congress ANC mai mulkin Afrika ta Kudu, ta bayyana aniyar kasar ta kauracewa kujerar zama mamba a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wato ICC.

Shugaban sashen hulda da kasashen waje na jam'iyyar ta ANC Obed Bapela, ya tabbatar da hakan bayan kammala taron koli na jam'iyyar.

Bapela ya ce, jamiyyar ta dauki wannan mataki ne yayin da ta lura cewar, ICC ba ta da alkibla, kuma ba ta mutunta dokoki da ka'idojin da aka gindaya yayin gudanar da ayyukanta.

Dangantaka ta fara tsami ne tsakanin Afrika ta Kudun da ICC tun lokacin da ICC ta gaza cika sharurrudan ba da sammacin kama shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir a yayin da yake halarta taron AU a birnin Johannesburg a tsakiyar watan Yunin shekarar nan.

A kwanan nan ma, Afrika ta Kudun ta bijirewa umarnin kama al-Bashir a yayin da ya ziyarci kasar, tana mai cewar, tana bin ka'idar ICC, kuma tana bin ka'idar AU.

A karkashin dokokin kungiyar ta AU, babu wani shugaba mai ci da za'a kama yayin da yake kasashen Afrika.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China