in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara yawan gurabe ga mata a taron NPC na 13
2017-03-09 10:23:10 cri

Kasar Sin za ta karawa mata adadin kujerun wakilci, a majalissar wakilan al'ummar kasar, wadanda za su halarci babban taron NPC karo na 13 da za a yi a badi.

Sauran sassan da ake sa ran za su samu karin wakilcin sun hada da ma'aikata, da manoma da kwararru a fannoni daban daban, kamar dai yadda wani daftari shawara da aka mikawa 'yan majalissun dokokin kasar domin su nazarta ya bayyana.

Daftarin ya ce bisa jimilla, ana fatan kara adadin mata wakilai da za a zaba daga matakan al'umma na kasa, ta yadda adadin su zai zarta na mahalarta taron NPC karo 12. Har wa yau za a kara yawan wakilai daga tsagin ma'aikata 'yan ci rani, yayin da kuma ake fatan rage yawa jami'an gwamnati da na 'yan jam'iyya.

Rahotannin baya sun nuna cewa, cikin wakilan NPC kusan 3,000 da suka halarci taro na 12, kaso 14 bisa dari ma'aikata ne da kuma manoma, adadin da ya karu da kusan sama da kaso 5 bisa dari, idan an kwatanta da mahalarta taron na 11.

A daya bangaren kuma, adadin kwararru shi ma ya karu, da sama da kaso 1 bisa dari. Sai kuma tsagin jami'an gwamnati da 'yan jam'iyya, wanda ya kai kusan kaso 35 bisa dari a taron na 12, adadin da ya ragu da kaso kusan 7 bisa dari idan an kwatanta da taro na 11.

Da yake karin haske game da daftarin shawarar ga 'yan majalissar dokokin dake zama na 5 na majalissar NPC ta 12 a jiya Laraba, mataimakin shugaban zaunannen kwamitin majalissar Wang Chen, ya ja hankalin wakilai da su tabbatar da bin doka da oda yayin zaben da za su yi, karkashin jagorancin JKS ta kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China