in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalissar dokokin Libiya ta yi Allah wadai da hari kan wasu cibiyoyin adana mai
2017-03-08 10:10:02 cri

Mai magana da yawun majalissar dokokin kasar Libiya mai helkwata a gabashin kasar Abdullah Belheg, ya ce majalissar ta yi Allah wadai da harin da mayakan sa kai na "Benghazi Defense Brigades" suka kai, kan wasu cibiyoyin adana mai dake gabashin kasar.

Mr. Belheg ya ce yayin zaman ta na jiya Talata, majalissar ta tattauna game da dauki ba dadin da dakarun sojin kasar suka yi da tsagin dakurun masu dauke da makamai a ranar Juma'a makon jiya. Ya ce, majalisar na daukar wannan farmaki na kungiyar "Benghazi Defense Brigades" a matsayin ta'addanci kan cibiyoyin adana albarkatun man kasar, ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su nuna adawar su da wannan lamari.

Tuni dai majalissar dokokin ta yanke kudurin dakatar da tattaunawar siyasa da ake yi, domin nuna bacin ran ta ga aukuwar wannan harin.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China