in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe sojoji 13 a filin albarkatun man fetur na Libya
2015-02-05 12:56:19 cri

Wasu 'yan tsagera sun kashe dakarun soji 13, tare da raunata wasu sojoji 8 a wani hari da aka kaiwa filin albarkatun man fetur na al-Mabruk dake kudancin kasar Libya

Wata majiyar hukumomin tsaro ta ce, an kashe sojoji 4 a wani harin kwantan bauna a filin albarkatun man fetur na al-Mabruk dake kudu maso gabashin birnin Sirte. Kakakin masu gadin filin Hakim Mazab al-Zwai ya ce, an hallaka sojojin ne a yayin da suke kan hanyarsu zuwa filin albarkatun man fetur din domin kai dauki ga masu gadin filin man.

Al-Zwai ya ce, sojojin sun isa wurin jim kadan bayan masu dauke da bindigogin sun kashe masu gadi tare da kwace filin albarkatun man fetur daga hannun masu gadi da suka hada da masu gadin filin 4, 'yan kasar Philipins 3 da kuma 'yan kasar Ghana 2, kuma ga baki daya an kashe mutane 13.

Mohammed al-Hrari, jami'in kamfanin man fetur na kasar Libya ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, babu wasu ma'aikata da aka sace a yayin da 'yan bindigan suka kai farmaki a kan filin albarkatun mai na al-Mabruk. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China