in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta kaddamar da hari ta sama kan shugaban al-Qaida da ke Libya
2015-06-15 11:23:03 cri

Hukumar tsaron Amurka ta Pengon ta bayyana cewa, sojojin Amurka sun kaddamar da hare-hare ta sama kan shugaban kungiyar al-Qaida da ke kasar Libya.

Kakakin hukumar ta Pengon Steve Warren wanda ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, ya ce, harin na ranar Asabar ya yi nasara, domin sojojin na Amurka sun tabbatar cewa, harin ya sauka a wurin da aka tsara.

An ruwaito gwamnatin Libya na tabbatar da cewa, jiragen yakin Amurka sun kaddamar da hare-hare ta sama tare da kashe Mokhtar Belmokhtar da wasu 'ya'yan kungiyar Ansar al-Shariah, reshen kungiyar ta al-Qaida a birnin Ajdabiya da ke gabashin kasar ta Libya.

Wannan harin na zuwa ne bayan da Amurka ta tattauna da mahukuntan na Libya. Sai dai ba tabbatar ba ko Amurkan ta yi amfani da jirage maras matuki ne ko kuma jiragen yaki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China