Sabon shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Mohamed da aka fi sani da Farmajo, ya karbi rantsuwar kama aiki a jiya Laraba, a wani biki da ya samu halartar shugabannin yankin gabashin Afrika, da suka yi alkawarin marawa sabuwar gwamnatin baya.
Shugabannin da suka halarci bikin da ya gudana a filin jirgin saman Mogadishu, sun hada da na kasashen Djibouti da Kenya da Sudan da Uganda da kuma Habasha.
Da yake jawabi yayin bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kasar na 9, Farmajo ya yi alkawarin dawo da martabar kasar dake kahon Afrika ta hanyar magance kalubalen tsaro da na tattalin arziki.
Farmajo wanda aka zaba a ranar 8 ga watan nan, ya kuma yi alkawarin ba batun tsaro muhimmanci, ya ce, gwamnatinsa za ta yi kokarin magance matsalolin fari da na tattalin arziki.
Ana ganin zaben Farmajo a matsayin wani ci gaba ga tsarin demokradiyyar kasar da ba ta samu ingantaccen shugabanci na bai daya ba tun bayan rushewar mulkin soji na Siad Barre a shekarar 1991. Al'amarin da ya haddasa yakin basasa da aka shafe shekaru da dama ana yi. ( Fa'iza Mustapha)