in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yan sandan Sudan sun killace wani gida a birnin Khartoum
2017-02-13 11:03:18 cri

Rundunar 'yan sandan kasar Sudan ta bayyana cewa, dakarunta sun yi nasarar gano wani abin fashewa da ya tashi a wani gida da ke birnin Khartoum, fadar mulkin kasar.

Wata sanarwa da rundunar ta rabawa manema labarai a jiya Lahadi ta bayyana cewa, abin fashewan ya tashi ne yayin da wani yake kokarin hada wani bam kiran gida wanda daga bisani ya tashi. Sai dai rundunar ta ce, kayayyakin da dakarun nata suka kwace a hannun wadannan bata gari ba masu matukar hadari ba ne.

Bugu da kari, rundunar 'yan sandan ta ce, ta samu kayayyakin hada abubuwan fashe da fasfon 'yan kasashen waje a wannan gida.

Wani shaidun gani da ido ya ce, ya ga 'yan sandan sun kama baki da ake zaton 'yan kasashen Syria, Somaliya da wasu kasashen Larabawa ne da tarin makamai da abubuwan fashewa. Kuma yanzu haka sun yiwa gidan kawanye bayan da aka ji karar wata fashewa.

Rahotanni na cewa, 'yan sanda sun kara tsaurara matakan tsaro a birnin Khartoum, tare da killace wurin da lamarin ya faru.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China