Wani kwamandan soji ya ce, a kalla baki 'yan asalin kasashen waje takwas aka kama, yayin aikin yaki da 'yan tada kayar baya da dakarun gwamnati ke yi a jihar Borno dake arewa maso gabashin Nijeriya.
Kwamandan dakarun dake yaki a jihar Borno Lucky Irabor ya shaidawa manema labarai a Maiduguri, babban birnin jihar cewa, an kama baki takwas da suka hada da 'yan kasar Chadi hudu, da 'yan Nijer uku, da kuma 'dan Kamaru guda daya, da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne.
Ya ce, yayin yaki da 'yan tada kayar bayan tsakanin 2 ga watan Fabreru da 1 ga wannan wata da muke ciki, dakarun sun kuma yi nasarar ceto mutane dubu bakwai da dari takwas da casa'in da takwas. (Fa'iza Mustapha)