Rundunar 'yan sandan jihar Legas, cibiyar kasuwancin tarayyar Najeriya, ta ce, ta kara tsaurara matakan tsaro, biyo bayan rahotannin karuwar sace mutane da ake samu a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Fatai Owoseni ya shaidawa manema labarai cewa, a watan Fabrairun da ya gabata, jami'ansa sun samu nasarar damke mutane 24 da ake zargi da aikata laifukan fashi da makami, baya ga wasu karin mutane 19 da ake zarginsu da sace mutane, sai kuma wasu mutane 8 da aka kama da ayyukan kungiyoyin asiri.
Rundunar ta kuma bayyana cewa, daga watan Disamban shekarar 2015 zuwa watan Nuwamban shekarar 2016 da ta gabata, mutane a kalla 246 ne suka gamu da ajalinsu, yayin da aka yi awon gaba da motoci 542, kana aka kama wasu mutane 486 da ake zaton 'yan fashi da makami ne a Legas din.
Bugu da kari, a cikin wannan lokaci da ake batu, rundunar 'yan sandan jihar ta samu rahotannin sace mutane 51, kana ta samu nasarar dakile aukuwar munanan ayyuka 179 a jihar, biyo bayan matakan gaggauwa da jami'an tsaro suka dauka.
Kwamishinan 'yan sandan ya baiwa mazauna jihar, da ma masu sha'awar zuba jari tabbacin cewa, rundunarsa tana daukar matakan tsaron da suka dace na ganin ta kare rayuka da dukiyoyinsu.
Shi ma gwamnan jihar ta Legas Akinwunmi Ambode ya baiwa mazauna jihar tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta kara tsaurara matakan tsaro wajen ganin an kare rayuka da dukiyoyinsu.(Ibrahim)