in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsadar kudaden haraji na matukar barazana ga kasuwanci a Ghana
2017-02-09 09:46:12 cri

Kungiyar masu masana'antu ta kasar Ghana AGI, ta fitar da wani rahoton na watanni 3 na karshen shekarar 2016, inda ta bayyana cewa, harkokin kasuwanci a kasar Ghana suna fuskantar barazana sakamakon ci gaba da kara kudaden bukatun yau da kullum a kasar.

Rahoton ya kuma ambato wasu karin kalubaloli da suka hada da tsadar kudaden da ake caza wajen ba da rance, da ninninka kudaden haraji, baya ga matsalar faduwar darajar kudin kasar Cedi, wadannan na daga cikin manya batutuwa dake kawo barazana ga harkokin cinikayya a kasar ta Ghana, in ji wannan rahoto.

Ratoton wanda ya auna kididdigar yadda ake gudanar da kasuwanci a kasar na watanni uku na farko, da na biyu, da kuma watanni 3 na karshen shekarar 2016, ya lura cewa, kashi 70 cikin 100 na harkokin kasuwancin kasar, ana sa ran zai iya samun tagomashi.

Wannan ya nuna cewa, an samu gagarumin ci gaba a harkokin kasuwancin na Ghana idan aka kwatanta da kashi 57 cikin 100 da ake samu a shekarun baya, rahoton ya kara da cewa, hasashen karuwar kasuwanci a kasar ya ragu daga 37 zuwa 26 kamar yadda aka yi hasashe a wannan lokaci.

Rahoton ya ce, tabbacin da ake da shi game da yiwuwar raguwar kasuwanci a kasar da kashi 6.2 zuwa kashi 3 cikin 100, rahoton ya ce, hasashen samun bunkasuwar kasuwanci da aka yi na kashi 99 a tsakanin watan Yuli zuwa Satumba ya karu zuwa kashi 101.6 cikin 100 a watanni 3 a karshe na 2016.

Ministan harkokin kasuwanci na kasar, Ibrahim Mohammed Awal, ya ce gwamnatin kasar za ta inganta dokokin da suka shafi gudanar da kasuwanci a kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China