in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana za ta karfafa dangantaka da kasar Sin
2017-02-06 09:42:17 cri

Ministan kudin Ghana Kenneth Ofori-Atta ya ce, sabuwar gwamnatin kasar ta sha alwashin karfafa dangantakarta da kasar Sin.

Ministan ya ce, gwamnatin kasar za ta gudanar da tattaunawa karo na biyu da jakadan kasar Sin a Ghana a yau Litinin, domin tattauna hanyoyin karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Da yake karin haske ga manema labarai, Ofori-Atta ya ce, makasudin tattaunawar da kasar Sin shi ne, don neman tallafin gwamnatin kasar Sin game da yadda gwamnatin Ghanan za ta samu damar farfado da tattalin arzikinta.

Ofori-Atta, wanda ake sa ran zai gabatar da kasafin kudin sabuwar gwamnatin kasar ta Ghana a watan Maris, ya bayyana cewa, tawagarsa za ta gudanar da tattaunawa da jami'an asusun ba da lamini na IMF wanda kasar ta kulla yarjejeniyar rance da shi na shekaru uku, inda wa'adinsa zai cika a watan Afrilun 2018.

Ya kara da cewa, tawagarsa, za ta tattauna da IMF domin nazartar irin alfanun da ake samu karkashin wannan shiri.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China