Kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar, ya karyata rahoton da kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar a baya bayan nan, wanda ke cewa, dakarun sojin kasar sun hallaka fararen hula 240, ciki hadda jarirai a jihar Borno, da kuma wasu mutanen su 177 dake goyon bayan kafuwar kasar Biafara.
Da yake mai da martani game da rahoton a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, Rabe Abubakar, ya ce rahoton na Amnesty soki burutsu ne kawai maras ma'ana. Ya ce, yana fatan al'umma za su yi watsi da daukacin rahoton, duba da cewa, a baya ma kungiyar ta Amnesty, ta sha fidda makamancin wannan rahoto, inda take zargin sojoji da sauran jami'an tsaron kasar da aikata laufuka, ba tare da wata gamsasshiyar hujja ba.
Kaza lika Rabe ya zargi Amnesty International da kitsa bayanai na kashin kai, domin cimma wata manufa ta daban, tare da yunkurin jefa shakku a zukatan 'yan Najeriya, game da irin ayyukan da sojojin kasar ke yi na kakkabe bata gari daga sassan arewa maso gabashin kasar.
Daga nan sai ya jaddada alkawarin rundunar sojin Najeriya, na ci gaba da aiki ba dare ba rana, domin ganin an cimma nasarar kakkabe bata gari, da ma sauran matsalolin tsaro dake addabar sassan kasar.(Saminu)