Kamfanin dillancin labaran Koriya ta Kudu ya ruwaito rundunar sojan kasar na cewa, da misalin karfe 7 da miniti 36 na safe, bisa agogon Koriya ta Kudu, Koriya ta Arewa ta harba wani abun da ba'a san mene ne ba a yankin Tongchang-ri na Pyonganpuk-do.
Kawo yanzu ba'a samu bayani dalla-dalla ba kan wannan harbi. Haka kuma rundunar sojan kasar na gudanar da nazari kan nau'in abun da Koriya ta Arewa ta harba, gami da tazarar tafiyarsa.
Tuni a ranar 12 ga watan Fabrairun bana, Koriya ta Arewa ta yi nasarar harba wani makami mai linzami mai cin matsakaici gami da dogon zango. (Murtala Zhang)