Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ya bayyana cewa, kasar ta daidaita kundojin makamanta na nukiliya, ta yadda za su iya daukar makamai masu linzami.
Kamfanin dillancin labaran kasar KCNA ya ruwaito shugaban a yau Laraba, yana bayyana hakan lokacin da ya gana da ma'aikata da masana nukiliyar kasar, inda ya ba su umarni su kara inganta shirin makaman nukiliyar kasar.
Shugaba Kim ya sake yiwa masanan jawabi game da kara fito da dabaru da fasahohin kera makamai masu linzami wadanda za su rika amfani da kundojin makaman nukiliya, musamman kirar kasar ta Koriya ta Arewa.(Ibrahim)