in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Senegal da Gambia za su kara karfafa dangantaka tsakaninsu
2017-03-03 12:39:33 cri

Kasashen Senegal da Gambia sun yanke shawarar kara karfafa dangantakar dake tsakaninsu ta hanyar gudanar da manya turakan tuntubar juna a kai-a kai.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tsakaninsa da takwaransa na Gambia Adama Barrow da ke ziyara a Dakar.

Shugaba Macky Sall ya ce, duba da karfin dangantaka dake tsakaninisu, kasashen biyu za su cimma yarjejeniyoyi da dama yayin ziyarar ta Adama Barrow.

Ya kuma sanar da cewa, kasashen biyu sun amince da kawo karshen safarar kayyayaki ba bisa ka'ida ba da ake yi a tsakaninsu, al'amarin dake kara ta'azzara matsalar rashin tsaro.

Da yake jawabi kan ciniki da safarar katako tsakanin kasashen biyu, shugaban na Senegal, ya ce, yana son kafa wata hukuma da za ta hana lalata dajin Casamance.

A nasa bangaren, shugabn kasar Gambia Adama Barrow, ya tabbatar da tattaunawar da ya yi da 'yan kasuwar kasarsa game da safarar katakon.

A cewarsa, kamata ya yi a tsaftace harkar cinikin katako tsakanin kasashen biyu.

Shugaban na Gambia dake ziyarar yini uku a Senegal ya isa Dakar, babban birnin kasar ne jiya da rana, inda ya samu tarba a filin jirgin sama daga takwaransa na Senegal Macky Sall. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China