in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A tsaurara matakan tsaro a Gambia gabanin ziyarar manzon MDD a kasar
2015-01-04 09:45:09 cri

Mahukuntan kasar Gambia sun tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Banjul, babban birnin kasar, sakamakon wani yunkurin juyin mulkin da wasu sojoji suka yi a kasar makon da ya gabata wanda bai yi nasara, yayin da kuma manzon MDD mai kula da yankunan yammacin Afirka Mohammed Ibn Chambas ke shirin kai ziyara kasar nan ba da dadewa ba.

An ga sojoji suna kai komo a kan titunan, tare da binciken ababan hawa a kan manyan titunan kasar, matakin da mazauna wurin suka bayyana a matsayin wani kokari na damke wadanda ake zargi da shirya juyin mulkin da Laftana kanar Lamin Sanneh ya kitsa wanda bai yi nasara ba.

Nan ba da dadewa ba ne manzon musamman na babban sakataren MDD Mohammed Ibn Chanbas zai ziyarar kasar ta Gambia a kokarin ganin an tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da ke yammacin Afirka.

Ana sa ran yayin ziyarar zai tattauna da jami'an kasar ta Gambia, sannan ya sanar da MDD game da yanayin tsaron da ake ciki a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China