in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Ghana ya gabatar da kashin karshe na wadanda yake son nadawa ministoci
2017-01-13 10:46:36 cri

Kwanaki biyar bayan an rantsar da shi, shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya gabatar da matakin farko na gwamnatinsa.

Akufo-Addo ya kammala zaben wadanda yake son nadawa minitoci, inda ya gabatar da sunayen mutane goma sha daya a karshe.

Wannan adadi, ya kawo adadin wadanda yake son nadwa ministoci zuwa talatin da shida.

Akufo-Addo, ya shaida yayin wani taron manema labarai a Accra cewa, an mika dukkan jerin sunayen ga majalisar dokokin kasar, inda ake jiran sahalewarta.

Ya ce, gwamnatinsa na da kudurin cika alkawurran da ta daukarwa al'ummar kasar Ghana, kuma ya yi imanin cewa, wadanda yake son nadawa, su ne mutanen da za su taimakawa gwamnatinsa ciyar da kasar gaba.( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China