Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna dake arewacin Najeriya Aghole Abeh, ya ce an aike da jami'an rundunar na musamman zuwa yankunan da ake fama da tashe tashen hankula, a wani mataki na tabbatar da kare rayukan al'umma.
Wannan mataki dai na zuwa ne bayan samun rahotannin sake barkewar rikici a yankin arewa maso yammacin jihar ta Kaduna. Mr. Abeh ya ce, dakarun rundunar za su tabbatar sun kakkabe wannan yanki daga ayyukan bata gari, wadanda ke yunkurin tada hankulan al'umma a jihar.
Kwamishinan 'yan sandan ya kara da cewa, ana ci gaba da sintiri da jiragen sama na musamman, domin sanya ido kan duk wata zirga zirga ta al'ummu a yankin na arewa maso yammacin jihar Kaduna, domin dakile ayyukan mahara dake kaiwa kauyukan yankin farmaki na ta'addanci. Ya ce, rundunar 'yan sanda ba za ta saurarawa duk wani mutum, ko wasu gungun al'umma dake da niyyar tada zaune tsaye ba.
Daga nan sai ya ja hankulan al'ummar jihar, da su rika sanya idanu kan duk wata bakuwar fuska, ko zirga zirgar jama'a da ba su amince da ita ba, su kuma tuntubi jami'an tsaro da zarar bukatar hakan ta taso.
Kimanin mutane 200 ne dai aka hallaka, a yayin tashe tashen hankula da suka auku a wasu sassa na kudancin jihar ta Kaduna daga karshen shekarar bara zuwa wannan lokaci, kamar dai yadda hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ta bayyana.(Saminu)