in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-moon ya yi kakkausan suka game da harin ta'addancin birnin Damascus
2016-06-12 13:00:24 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya yi Allah wadai da harin ta'addanci da aka kaddamar a kusa da wurin ibada mai suna Sayidda Zeinab, wanda ke wajen birnin Damascus na kasar Syria, harin da ya sabbaba rasuwar mutane da dama, ciki hadda mata da kananan yara.

Mr. Ban wanda ke nuna takaicin sa ta bakin kakakin sa, ya ce, a kalla mutane 12 ne harin na tagwayen bama bamai ya hallaka, tuni kuma kungiyar ISIL ta bayyana daukar alhakin kaddamar da shi.

Babban magatakardar MDDr ya ce, dole ne a hukunta wadanda suka aikata wannan ta'asa. A hannu guda kuma, ya mika sakon ta'aziyya a madadin MDDr ga iyalai da 'yan uwan wadanda suka rasa rayukan su, tare da fatan samun sauki ga iyalan wadanda suka jikkata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China