in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin diplomasiyyar Sin da Amurka za su shirya zuwan Obama a Beijing cikin hadin gwiwa
2014-10-13 10:39:58 cri

Kasashen Sin da Amurka sun nuna amincewarsu a ranar Lahadi wajen aiki tare ta yadda za su shirya sosai kan zuwan shugaban Amurka Barack Obama a Beijing a cikin wata mai zuwa domin taron shugabannin tattalin arziki na hadin gwiwar tattalin arziki na Asiya da Pacifik (APEC). An cimma wannan yarjejeniya tsakanin ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, dake a yanzu haka yake rakiyar faraministan kasar Sin Li Keqiang a wata ziyarar aiki a kasar Rasha, da kuma sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a yayin wata hira ta wayar tarho bisa shawarar shugaban diplomasiyyar na Amurka. Mista Wang da Kerry sun amince da cewa, musammun ma bangarorin biyu za su shirya sosai domin ganawa tsakanin shugabannin kasashen biyu a yayin taron APEC da aka tsai da shirya a ranakun 10 da 11 ga watan Nuwamba, bisa yunkurin kara yaukaka sabon salon dangantaka tsakanin manyan kasashe masu muhimmanci da ya kamata Sin da Amurka su gina tare. Haka kuma sun tattauna kan shirin shawarwarin batun nukiliya na Iran, tare da bayyana niyyarsu ta cigaba da musanyar ra'ayi sosai kan wannan batun, ta yadda za'a samar da kwarin gwiwa ga dukkan bangarorin da abun ya shafa wajen mai da hankali kan burin cimma wata yarjejeniya daga dukkan fannoni. Shawarwari kan batun nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya shida da suka hada da Amurka, Burtaniya, Sin, Rasha, Faransa da Jamus za su yunkurin kai ga cimma wata yarjejeniya nan da ranar 24 ga watan Nuwamba. Shugabannin biyu, sun yi kuma musanyar ra'ayoyi kan hada kokarinsu tare domin taimakawa kasashen yammacin Afrika wajen yaki da cutar Ebola. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China