An daddale yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tsakanin Sin da Koriya ta Kudu a hukunce
A yau Litinin daya ga watan Yuni, a birnin Seoul, hedkwatar kasar Koriyar ta Kudu, ministan kasuwanci na Sin, Gao Hucheng, da ministan albarkatu da kasuwanci da masana'antu na Koriya ta Kudu, Yoon Sang- jick suka rattaba hannu kan yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci tsakanin Sin da Koriya ta Kudu a hukunce a madadin gwamnatocin biyu.
Wannan ne ya zama yarjejeniyar da ta kunshi batutuwa mafi yawa, da kuma shafar jimillar kudi mafi yawa da Sin ta daddale da wata kasar waje a fannin cinikayya cikin 'yanci, abinda zai kawo ma kasashen biyu moriyar sosai.
Haka kuma a litinin din nan har wa yau shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwararsa ta Koriya ta Kudu madam Park Geun-hye suka mika wa juna sakon murna a sakamakon wannan yarjejeniya.(Fatima)