in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon MDD game da batun Syria zai gana da kwamitin sulhun MDD
2016-02-26 09:25:10 cri

A yau ne ake sa ran manzon musamman na MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura zai yiwa kwamitin sulhun na MDD bayani game da tattaunawa kai tsaye da ya shirya tsakanin gwamnatin Syria da bangaren 'yan adawa.

Kakakin MDD Stephane Dujarric wanda ya bayyana hakan ga taron manema labarai a jiya Alhamis ya ce, bayan sanar da sabuwar ranar tattaunawa tsakanin sassan biyu, ana kuma sa ran De Misturan ya gana da manema labarai a birnin Geneva na kasar Switzerland.

A ranar 29 ga watan Janairun wannan shekarar ce, sassan biyu suka gana a birnin Geneva, karkashin kulawar MDD. Kana a ranar 3 watan Fabrairu, De Mistura ya dakatar da tattaunawar ta wucin gadi, sannan ya sanya ranar 25 ga watan na Fabrairu domin sake komawa teburin sulhu game da rikicin siyasar kasar ta Syria.

Amma daga bisani ya nuna shakku game da yiwuwar tattaunawar ranar 25 ga watan na Fabariru, saboda zargin da sassan biyu wato gwamnatin Syria da banganren 'yan adawar kasar ke yi juna na wargaza tattaunawar zaman lafiyar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China