in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dattijai a Nijeriya ta bukaci rundunar soji game da ayyukanta a nan gaba
2017-01-19 10:17:49 cri

Majalisar dattijai ta Nijeriya, ta shawarci rundunar sojin kasar da ta rika takatsantsa wajen gudanar da ayyukanta.

Yayin zaman majalisar na jiya, shugaban majalisar Ahmed Lawal, ya bayyana damuwa game da harin aka kai bisa kuskure kan fararen hula a jihar Borno.

Ahmed Lawal ya ce, mutane da dama sun mutu sanadiyyar harin da jirgin yakin soja ya kai kan sansanin 'yan gudun hijira na Rann, dake karamar hukumar Kala Balge na jihar Borno, a yankin arewa maso gabashin kasar.

Mataimakin shugaban majalisar Ike Ekeremadu, da ya jagoranci zaman, ya bukaci rundunar sojin kada ta bari wannan mummunan al'amari ya sanyaya gwiwarta, daga ci gaba da aikin da take.

Ya ce, suna fata da kuma addu'ar hakan ba zai kuma faruwa ba, yana mai bukatar rundunar sojin, musammam ta sama, da ta yi kokarinta wajen ganin al'amarin bai maimaita kansa ba.( Fa'iza Mustapha )

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China