in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsohon firaministan Somaliya ya zama shugaban kasar
2017-02-09 10:13:22 cri

Tsohon firaministan kasar Somaliya Mohamed Abdullahi Farmajo, shi ne mutumin da aka zaba a matsayin sabon shugaban kasar bayan da shugaban kasar mai ci Hassan Sheikh Mohamud, ya amince da shan kaye bayan zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Farmajo, wanda ya samu kuri'u 184 sama da abokin hamayyar tasa Sheikh Mohamud, wanda ya samu kuri'u 97 a zagaye na biyu, ya zama sabon shugaban kasar. Dan takara na uku shi ne tsohon shugaban kasar Sharif Sheikh Ahmed, wanda ya samu kuri'u 45.

Shi dai Farmajo, ya kasance firaministan kasar ne a lokacin gwamnatin rikon kwaryar kasar tsakanin shekarar 2009 zuwa 2010, an yabawa tawagar jami'an gudanar da zaben kasar saboda gudanar da zaben cikin nasara.

Tsohon firaiministan wanda kuma farfesa ne na jami'a ya fafata da 'yan takara 21 a lokacin zaben, inda ya yi galaba a kansu, hakan zai ba shi damar darewa a shugabanncin kasar na tsawon shekaru 4 masu zuwa.

Farmajo wanda yake da takardar zama na Amurka, ya samu digirinsa na biyu a bangaren kimiyyar siyasa daga jami'ar jihar New York dake Buffalo, kana a baya ya yi aiki a jihar New York ta Amurka, har ma da majalisar mulki ta yanki Buffalo, da sashen raba damammakin aiki, da kuma sashin kula da zirga zirga na birnin New York na Amurka.

An nada shi firaministan kasar a shekarar 2009 a lokacin mulkin shugaban kasar Ahmed inda ya maye gurbin firaministan kasar Omar Abdirashid Ali Sharmarke, wanda ya yi murabus daga mukamin nasa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China