in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya: An yi kira ga sassan jihar Galmudug da su warware sabani ta hanyar tattaunawa
2017-01-13 09:59:54 cri

Jakadun kasashe da na hukumomin kasa da kasa dake aiki a Somaliya, sun yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki a siyasar jihar Gulmudug, da su yi kokarin warware banbance banbancen dake tsakanin su ta hanyar tattaunawa.

Cikin wata sanarwa da suka fitar a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar ta Somaliya a jiya Alhamis, wakilan MDD, da na kungiyar tarayyar Turai ta EU, da takwarorin su na kungiyar AU, sun nuna damuwa game da sabanin da ya barke tun a farkon makon nan, tsakanin wakilan majalissar dokokin al'ummar jihar ta Galmudug da jagoran gwamnatin jihar Abdikarim Guled.

Wakilan sun ja hankalin daukacin sassan jihar, ciki hadda bangaren jami'an tsaro, da su maida hankali wajen daukar matakan da ka iya karfafa nasarorin da aka cimma game da kammalar zaben yankin, da ma kokarin da ake yi na ginin kasar ta Somaliya baki daya. Kaza lika sanarwar ta yi kira gare su, da su kaucewa daukar matakai da ka iya gurgunta ci gaban da aka samu a fadin kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China