in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU tana horas da jami'an sojoji dake Somaliya dokokin kare hakkin bin-Adam da daidaiton Jinsi
2017-02-21 20:28:36 cri
Tawagar kungiyar tarayyar Afirka dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya (AMISON) ta bude wani shirin horas da jami'anta dokokin MDD game da daidaiton jinsi da kare hakkin bil-Adama.

Manufar shirin samun horon na kwanaki uku, ita ce ilimantar da sojojin dake aiki karkashin inuwar tawagar AMISON har ma da sojojin kasar Somliya sanin nauyin da ke kansu gami da daidaita dukkan batutuwan da suka shafi jinsi daga dukkan fannoni.

Jami'in kula da harkokin da suka shafi jinsi a tawagar AMISON manjo Bupe Chanda ya bayyana a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya cewa, kwas din zai taimaka wajen kawo karshen yadda sojoji ke cin zarafin mata da take hakkin bil-Adama, kana su kasance jakadun tawagar AMISON na kwarai a yayin da suke gudanar da ayyukansu. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China