in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Somaliya 8 sun hallaka a fafatawa da mayakan Al-Shabaab
2017-02-13 10:21:26 cri
A kalla sojojin kasar Somaliya 8 ne aka kashe, kana wasu da dama suka jikkata a jiya Lahadi bayan wani gumurzu tsakanin mayakan Al-Shabaab da dakarun sojin na Somali (SNA) a yankunan Warmahan da Tihsile dake kudancin kasar ta Somalia.

Mataimakin gwamnan yankin Lower Shabelle mai kula da al'amurran kudi, Abdulfatah Abdullah Yusuf, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu manyan kwamandojin SNA su biyu na daga cikin wadanda aka kashe.

Abdullah ya ce, mayakan Al-Shabaab sun kaddamar da harin ne a barikokin sojojin na SNA dake Warmahan da Tihsile a shiyyar Lower Shabelle a safiyar Lahadi data gabata, bayan barkeawar fadan an kashe sojojin SNA 8, kana an kashe biyu daga cikin mayakan na Al-Shabaab da kuma jikkata wasu da dama.

Mataimakin gwamnan ya ce, harin wani salo ne na kwanton bauta da mayakan yan ta'addan suka kaddamar da safiyar wannan rana.

Yace an hallaka kwamandojin sojin biyu ne a wani bom da aka dasa a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen bataliyar sojojin domin agaza musu wadanda mayakan na Al-shabab suka yi musu kawanya.

Tuni dai kungiyar ta Al-Shabaab ta dauki alhakin kaddamar da harin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China