in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu sakamakon harin da aka kai a kwalejin horar da 'yan sanda na Pakistan ya karu zuwa 59
2016-10-25 13:54:42 cri

Rahotanni daga kasar Pakistan na cewa, yawan mutanen da suka mutu sakamakon harin da aka kai jiya da dare a kwalejin horar da 'yan sanda a birnin Quetta, hedkwatar jihar Balochistan da ke kudu maso yammacin kasar ya karu zuwa 59, yayin da wasu 117 suka jikkata.

Firaministan kasar Pakistan Mian Muhammad Nawaz Sharif ya yi Allah wadai da wannan hari, yana mai cewa, harin ta'addancin ba zai canza aniyar Pakistan ta yaki da ta'addanci ba. Har yanzu dai babu wata kungiyar da ta yi shelar daukar alhakin kai wannan harin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China