Tuni dai majalisar wakilan Najeriyar ta kafa wani kwamiti wanda zai gudanar da bincike game da dalilan dake haddasa bullar cutar da kuma yadda za a shawo kanta, kana kwamitin zai mika rahotonsa nan da makonni 6 domin daukar makatai na gaba.
Sergius Ogun, dan majalisar wakilan kasar ne, shine ya sanar da wannan batu , inda ya bayyana damuwa kan bullar cutar wanda tuni ta bazu a jahohin kasar 26 da kuma birnin tarayya.
A cewarsa, matsalar bullar cutar ta haifar da gagarumar hasara ga masu kiwon kaji, kuma zata iya zama barazana ga lafiyar masu amfani da naman kajin.
Dan majalisar yace matukar ba a kai ga gano musabbabin dake haifar da cutar ba, akwai yiwuwar zata iya sake bulla a nan gaba.
A kalla kaji dubu 80 ne suka kamu da cutar murar tsuntsayen a gidajen gona 45 a jahar Kano a watan Janairun shekarar 2016.