Shehu Bawa, wanda shi ne Daraktan sashen kula da lafiyar dabbobi na ma'aikatar aikin gona dake jihar, ya shaidawa manema labarai a Kano cewa, tuni gwamnati ta amince da fitar da kudin sayan sinadaran.
Ya ce sashen na sa, ya kuma kara kaimi wajen sanya idanu a dukkan kasuwanni, domin tabbatar da ba a sayar da kajin da suka kamu da cutar ga jama'a.
Shehu Bawa ya kara da cewa, gwamnatin tarayya ta yi alkawarin biyan diyya ga wadanada aka samu barkewar cutar a gonakinsu tsakanin shekarun 2014 da 2015 da kuma 2015 zuwa 2016.
Sama da tsuntsaye dubu tara aka kashe a jihar, tun daga lokacin da aka samu barkewar cutar a ranar 15 ga watan Decemban da ya gabata. ( Fa'iza Mustapha)