A wajen babban taron WHO karo na 140 da aka yi, Madam Margaret Chan ta yi nuni da cewa, tun daga watan Nuwamban bara, akwai kasashe da yankuna kusan 40 wadanda suka bada rahotannin cewa, sun gano annobar mura mai hadarin gaske tsakanin kaji da agwagin da ake kiwonsu a gida, gami da tsuntsayen daji, abun da ya sa hukumar WHO ta yi kira da a dauki matakan kare yaduwar annobar zuwa yankuna daban-daban.
Madam Margaret Chan ta kara da cewa, tun bayan barkewar annobar murar tsuntsaye mai nau'in H1N1 a shekara ta 2009 gami da 2010, kasashe suka daura damarar dakile yaduwar cutar a fadin duniya, sai dai ta ce, da sauran rina a kaba.
Chan ta jaddada cewa, bisa tanadin ka'idojin kiwon lafiya na duniya, idan aka gano dan Adam wanda ya kamu da cutar murar tsuntsaye, kamata ya yi a bada rahoto ba tare da bata lokaci ba, saboda 'rigakafi ya fi magani'.(Murtala Zhang)