in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Minista: Najeriya za ta bunkasa yanki mai arziki mai
2017-02-12 11:58:54 cri
Gwamantin Najeriya tana yi bakin kokarinta domin aiwatar da muhimman ayyukan raya ci gaba da kuma tabbatar da zaman lafiyar yankin Niger Delta mai arzikin mai.

Ministan ma'aikatar kula da yankin Niger Delta Usani Usani, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin taron masu ruwa da tsaki a yankin, yayin da mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osibanjo ya ziyarci jahar Bayelsa.

Mataimakin shugaban kasar ya jagoranci tawagar ministoci, da shugabannin ma'aikatau da sauran kusoshin gwamnati zuwa jahar, a matsayin wani yunkuri da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi na lalibo hanyoyin wanzar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.

Mata, matasa, sarakunan gargajiya, shugabannin kamfanoni, da masu rike da mukaman siyasa da ma sauran masu rike da mukaman gwamnati, sun shiga cikin wannan tattaunawar da aka gudanar.

Ministan ya ba da tabbacin gwamnatin kasar na maida hankali wajen samar da ayyukan raya ci gaban yankin, ya kara da cewa gwamnatin kasar tana jin takaici game da irin halin da yankin na Niger Delta ke ciki.

Ya jaddada bukatar yankin ya hada kai da gwamnati, kasancewa jahar Bayelsa da yankin kudu maso kudu suna da matukar kima a idon gwamnati. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China