in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan Najeriya sun karbe iko da kamfanin jiragen sama na Arik
2017-02-10 09:29:56 cri
Karamin ministan sufurin jiragen sama a Najeriya Hadi Sirika, ya ce gwamnatin kasar ta amshe iko da kamfanin jiragen sama na Arik, sakamakon dinbin bashi da ya yiwa kamfanin katutu.

Arik dai shi ne kamfanin sufurin jiragen sama na cikin gida mafi girma a Najeriya, sai dai kuma a baya bayan nan ya shiga wani hali na kaka ni ka yi, ta yadda idan har ba a dauki matakan gaggawa ba, zai iya kaiwa ga durkushewa baki daya.

Da yake karin haske game da daukar wannan mataki, kakakin hukumar dake lura da kadarori a Najeriyar AMCON Mr. Jude Nwauzor, ya ce hukumar ce za ta lura da sha'anin kamfanin a hukunce, kuma an dauki matakin ne domin tabbatar da kamfanin bai karasa durkushewa ba.

Kamfanin Arik dai na sufurin fasinjoji a cikin kasar, wanda bisa kididdiga aka yi imanin cewa, yana daukar kaso 55 bisa dari na jimillar fasinjojin dake hawa jiragen sama a cikin kasar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China