in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AMISOM za ta binciki zargin kisan fararen hula a Somaliya
2017-01-09 10:33:11 cri

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar tarayyar Afirka ko AMISOM a takaice, ta sha alwashin gudanar da bincike game da zargin da ake yiwa dakarun ta, na kisan fararen hula ranar Juma'a a yankin Barawe dake kudancin kasar Somaliya.

Rahotanni sun bayyana cewa, fada ya barke tsakanin sojojin da wasu mahara, a wani wuri dake tsakanin Marangway da Jameeko dake wajen garin Barawe, yayin da rukunin sojojin ta AMISOM ke rangadi. An ce, da farko wata nakiya da aka binne ce ta tashi, kafin daga bisani wasu mahara su aukawa sojojin, matakin da ya tilasta masu maida martani da bindigogi.

Sai dai sabanin bayanan da wasu kafafen watsa labarai ke yadawa, tawagar ta AMISOM ta ce ba ta da wata masaniya ta rasuwar fararen hula, amma duk da haka za ta gudanar da bincike domin tantance hakikanin abun da ya faru, da ma matakin da ya dace a dauka a nan gaba.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China