in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama mutane 6 da ake zargin 'yan Al-Shabaab dangane da fashewar bam a Somaliya
2016-03-01 09:26:19 cri

Rundunar tsaro a Somaliya ta kama wadansu mutane 6 da ake zargin 'yan kungiyar Al-shabaab ne a ranar Litinin din nan dangane da mummunan fashewar bam har biyu a garin Baidoa dake kudancin kasar Somaliya.

Abdullahi Ali Watin, kwamishinan yanki na garin Baidoa ya shaida wa manema labarai cewa, jami'an tsaron sun aiwatar da gaggarumin samame a kan 'yan ta'addan a cikin wannan gari, inda suka kame guda shida da ake kyautata zaton 'yan Al-Shabaab ne, kuma suke da hannu a mummunan fashewar bam har biyu.

Dakarun 'yan kungiyar ta Al-Shabaab sun kai harin bama-bamai a wani taron jama'a da aka yi a tsakiyar garin na Baidoa a ranar Lahadin da ta gabata, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 30, sannan wadansu guda 42 suka samu raunuka.

Gwamnatin kasar ta Somaliya da tawagar wanzar da zaman lafiya ta kungiyar AU dake kasar dai tuni suka soki wannan harin.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China