in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Za a samar da karin cibiyoyin cajin ababen hawa masu amfani da lantarki
2017-02-10 09:18:55 cri
Hukumar dake kula da makamashin ta kasar Sin ko NEA a takaice, ta ce a bana za a samar da karin wuraren cajin motoci masu amfani da lantarki 800,000, ciki hadda 100,000 domin al'umma, a wani mataki na tabbatar da wadatar cibiyoyin cajin ababen hawa na lantarki.

A cewar hukumar ta NEA, a bara an samar da irin wadannan wurare na caji har 100,000, wanda hakan ya sanya adadin su kaiwa ga 150,000.

A bara irin wannan nau'i na ababen hawa da aka yi amfani da su cikin kasar ta Sin, sun zuki lantarki da ya kai na sa'o'i daidai da kilowatt biliyan 1.2, matakin da ya bada damar tsumin man fetur da ake konawa har tan 400,000.

Bisa tanajin shirin shekaru biyar-biyar na kasar Sin, wato tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020, an tsara gina cibiyoyin cajin ababen hawa masu amfani da lantarki a sassa daban daban, wadanda za su ishi ababen hawa miliyan 5 nan da shekara ta 2020. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China