in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kafa wuraren da motoci za su rika yada zango guda 2000 nan da shekara 2020
2016-11-10 09:21:14 cri

Mahukuntan kasar Sin sun bayyana shirinsu na gina wuraren da motoci za su rika yada zango guda 2000 nan da shekarar 2020, a wani mataki na karfafa yin bulaguro ta hanyoyin mota.

Hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta kasar tare da hadin gwiwar wasu sassan ma'aikatu guda 10 ne suka gabatar da matakan aiwatar da wannan shiri a jiya Laraba, inda suka yi kira da a kafa wuraren da motoci za su rika yada zango a matsayin hanyar bunkasa sashen yawon bude ido na cikin gida.

A cikin shekaru biyu da suka gabata, an samu bunkasuwar kamfanonin samar da hidima ga masu yawon shakatawa, wadda ta kai kai kaso 85 cikin 100 a ko wace shekara.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China