Gwamnatin kasar Sin ta bayyana cewa, daga yanzu zuwa shekarar 2020, za ta samar da sabbin motoci masu amfani da wutar lantarki miliyan 2 da ta saba kerawa a ko wace shekara.
Ministan masana'antu da fasahohin sadarwa na zamani Miao Wei ne wanda ya bayyana hakan a karshen mako a wani dandalin da aka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya ce, ya zuwa shekarar 2025, cikin motoci biyar da za a sayar a kasar Sin, a kalla guda mai amfani da wutar lantarki ce.
Minista Miao ya kara da cewa, gwamnati za ta ci gaba da inganta manufofi da harkokin bincike, da matakan zuba jari a bangaren gina tashoshin cajin irin wadannan motoci, da bunkasa hadin gwiwa tsakanin sauran kasashen duniya, ta yadda za a raya wannan sashe.
Alkaluma na cewa, a shekarar 2016, kasar Sin ta kera sabbin motoci masu amfani da wutar lantarki 517,000. Kuma tun a shekarar 2015, kasar ta Sin ke kan gaba a duniya a fannin kera irin wadannan motoci da ba sa gurba muhalli. Ya zuwa yanzu, ta sayar da irin wadannan motoci sama da miliyan 1.(Ibrahim)