Ma'aikatar al'adu ta kasar Sin tare da ma'aikatar kudi za su hada hannu waje daya domin habaka wurare na musamman a bangaren masana'antun al'adu.
Kasar Sin za ta karfafa kokarinta a bangaren taimakon kudi, kafa shirye-shirye, da kuma jawo hankalin al'umma daga kasashen waje wajen kawo ziyara domin inganta tarihi da al'adun wasanni, kamar yadda aka sanar cikin wata takardar jerin shirye-shirye na ma'aikatun biyu a ranar Talatan nan.
Sin za ta mai da hankali a kan shigar da al'adun kasar a wajen gina birane da taimakon tsarin gine-gine na wuraren kasuwanci wanda zai nuna yanayin gidajen na karkara.
Kasar ta Sin har ila yau za ta ba da kwarin gwiwwa a kwalejoji, cibiyoyin bincike da hada-hadar ciniki da zai inganta hadin gwiwwa da kasuwannin cikin gida, in ji takardar jerin shirye-shiryen. (Fatimah)