in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Somaliya na bukatar dala miliyan 864 don samar da agaji
2017-01-03 10:29:28 cri

Kungiyoyin ba da agaji ta kasa da kasa dake aiki a Somaliya suna bukatar zunzurutun kudi da yawansu ya kai dala miliyan 864 domin tallafawa mutane miliyan 3.9 wadanda ke bukatar agajin gaggawa nan da karshen shekarar nan ta 2017.

Ofishin kula da al'amurran jin kai na MDD (OCHA) ya sanar a jiya Litinin, game da sabon shirin ba da agaji na MDD a Somaliya na shekarar 2017.

A cewar OCHA, sabon shirin ya kunshi dabarun aikin jin kai a Somaliya na shekaru 3, wato daga shekarar 2016 zuwa 2018, shirin na shekarar 2017 yana da aniyar ceto rayukan al'umma, tabbatar da ba da kariya ga mutanen da ba su da galihu, tallafawa aikin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, da inganta rayuwar al'umma.

A cewar wani rahoton da MDD ta fitar a farkon wannan shekarar, mutane miliyan 5 a Somaliya, wato sama da kashi 40 cikin 100 na al'ummar kasar ne ke fama da matsalar karancin abinci.

Rahoton ya nuna cewa, a kalla yara dubu 300 'yan kasa da shekaru 5 ne ke fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki, kuma daga cikin adadin, yara dubu 50 ne matsalar ta fi kamari a kansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China