Jiya Talata aka kaddamar da bikin nuna al'adun kasar Sin a kasar Kamaru, za a shafe kwanaki uku ana gudanar da bikin, kuma majalisar dokokin kasar ta Kamaru da ofishin jakadancin kasar Sin suka shirya wannan bikin cikin hadin gwiwa, kana tawagar sada zumunta tsakanin Sin da Kamaru ta majalisar dokokin Kamaru, da kwalejin koyar da Sinanci ta Confucius ta jami'ar Yaounde ta biyu, da tawagar likitocin da kasar Sin ta tura wa kasar ta Kamaru su ma suna gudanar da bikin tare.
Yayin bude bikin, mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Kamaru Datouo Theodore ya gabatar da wani jawabi, inda ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Kamaru a fannonin likitanci, da kuma al'adu yana kara zurfafuwa a kai a kai, tawagar sada zumunta tsakanin Sin da Kamaru ta majalisar dokokin Kamaru tana taka muhimmiyar rawa wajen kara karafafa hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu, kana ta samar da wani dandalin sada zumunta da fahimtar juna dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu.
Theodore ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta samu babban sakamako wajen raya tattalin arziki, har ya jawo hankalin jama'ar kasashen duniya, Kamaru ita ma haka take, shi ya sa tana son koyon fasahohi daga kasar Sin, domin cimma burinta na kasance wata kasa mai saurin samun ci gaban tattalin arziki nan da shekarar 2035.
Jakadan kasar Sin dake Kamaru Wei Wenhua ya bayyana cewa, shekarar 2016 shekara ta cika shekaru 45 da aka kafa huldar diplomasiya dake tsakanin Sin da Kamaru, a cikin wadannan shekaru 45 da suka gabata, sassan biyu sun tafiyar da huldar yadda ya kamata, yanzu dai kasar Sin ta riga ta kasance kasa ta farko wajen yin ciniki da Kamaru. Kana Wei Wenhua yana fatan bikin nuna al'adun kasar Sin zai samar da damammaki ga al'ummar Kamaru da su kara fahimtar kasar Sin, tare kuma da kara sada zumunta dake tsakanin al'ummomin kasashen biyu.(Jamila)