in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yiwa 'yan gudun hijirar Najeriya kusan 74,000 rajista a Kamaru
2016-11-04 09:45:45 cri

Babbar jami'ar tsare tsare, kuma wakiliyar shirin samar da ci gaba na MDD a kasar Kamaru Najat Rochdi, ta ce ya zuwa watan Oktobar da ya gabata, kimanin 'yan gudun hijirar Najeriya 74,000 ne aka yiwa rajista a kasar Kamaru. Hakan a cewar ta ya biyo bayan karuwar masu gujewa rikicin kungiyar Boko Haram ne daga Najeriya.

Jami'ar ta ce, masu neman mafakar na zaune ne a sansanonin Minawa dake yankin arewa mai nisa, yankin da tun daga shekarar 2013, ke fuskantar hare hare a kai a kai daga mayakan kungiyar ta Boko Haram.

Rahotanni na nuna cewa, tun bayan kafuwar tawagar hadin gwiwar sojojin Najeriya, da Nijar, da Kamaru, da Chadi, da Benin a farkon shekarar bara, an samu sassauci game da ayyukan tada kayar baya da mayakan Boko Haram ke gudanarwa a kasar ta Kamaru.

Amma fa a hannu guda, ci gaba da aukuwar hare haren kungiyar a arewa maso gabashin Najeriyar, na tilasawa daruruwan 'yan kasar tserewa zuwa kasar ta Kamaru. An ce a shekarar 2015, adadin 'yan gudun hijirar Najeriya a Kamaru sun kai mutane kusan 60,000.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China