in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe na kokarin cimma matakin MDD na tunkarar cutar kanjamau
2017-02-09 09:52:56 cri

Wani babban jami'in hukumar yaki da cutar kanjamau na Zimbabwe, ya ce kasar na kokarin cimma matakin kula da cutar kamar yadda MDD ta sanya.

Matakin na MDD na da nufin kara yawan adadin mutanen da suka san suna dauke da cutar, da wadanda ke karbar magani, da kuma wadanda magani ke rage tasirin cutar a jikinsu, zuwa kashi casa'in casa'in casa'in cikin dari.

Daraktan hukumar mai kula da sahsen bibiya da tantance tasirin cutar Amon Mpofu, ya shaidawa manema labarai cewa, wasu gudunmomi goma dake kasar sun ma zarce matakin da ake son cimmawa.

Ya ce, kimanin al'ummar kasar miliyan daya da dubu dari biyu ne ke dauke da cutar, kuma kashi 74.2 cikinsu sun sani, sannan kashi 86.8 daga ciki na karbar magani.

Mpofu ya kara da cewa, suna da yakinin yaki da cutar, ta yadda ba za ta ci gaba da zama barazana ga lafiyar al'umma ba. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China