in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta fitar da kudin bashin kasa
2016-11-28 11:21:10 cri

Jiya Lahadi babban bankin kasar Zimbabwe ya sanar da hotunan kudaden bashin kasa da za ta fitar, kuma ya bayyana cewa, ya riga ya yi aikin share fage har tsawon watanni shida, kuma zai fitar da kudaden a yau ranar 28 ga wata a hukunce.

Babban bankin Zimbabwe ya bayyana cewa, kudaden bashin kasa da Zimbabwe za ta fitar suna kumshe da kudade iri guda uku wato takardar kudin yuan 2 da na yuan 5, da cent yuan 1, darajarsu za ta yi daidai da ta dalar Amurka, kuma za a yi amfani da su a fadin kasar.

Kafin wannan, shugaban babban bankin kasar ya taba bayyana cewa, kafin karshen bana, bankinsa zai fitar da kudaden bashin kasa da yawansu zai kai kai yuan miliyan 65 a kasar.

A karshen watan Oktoban bana, shugaban kasar ta Zimbabwe Mugabe ya sa hannu kan wata doka, wadda ta samar da tushen doka ga aikin fitar da kudaden, inda dokar ta tanada cewa, ko gwamnatin kasar, ko kamfanoni a kasar, ko jama'ar kasar, bai kamata ba su ki amfani da wadannan kudaden bashin kasa da za a fitar da su.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China