in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Mugabe ya zargi wani fadan coci da neman tayar da rikici a kasar
2016-07-20 10:54:31 cri

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya yi Allah-wadai da matakin jagoran masu boren nuna adawa da gwamnati Evan Mawarire wanda ya durkusar da harkokin kasuwancin kasar makonni biyu da suka gabata ta hanyar kafofin sada zumunta.

Shugaba Mugabe ya yi zargin cewa, wasu ne daga kasashen ketare ke marawa fadan Evan Mawarire da mukarrabansa baya domin yiwa gwammatinsa zagon kasa.

Da yake jawabi, tsohon sakataren fadar shugaban kasar Zimbabwe Charles Utete ya ce, shugaba Mugabe bai yiwa Mawarire adalci ba, a don haka ya gargadi jama'a da su rika yin taka tsantsan domin kada wasu su fake da rigar addini su kai su su baro.

Ya ce, yana fatan Mawarire zai fadakar da jama'a bukatar zaman lafiya maimakon neman tayar da hankali a cikin kasa.

Shi dai fada Mawarire ya bukaci jama'a ne ta kafofin sada zumunta na zamani da su zauna a gidajensu, abin da ake ganin a matasyin zanga-zanga mafi girma da aka taba shiryawa a kasar tun shekarar 2005. A kuma ranar Talatar da ta gabata ne aka kama shi inda ake zarginsa da neman tayar da hankali.

Yanzu haka dai Mawarre yana kasar Afirka ta kudu, amma ya yi alkawarin cewa, nan ba da dadewa ba zai koma gida.

Sai dai wasu na rade-raden cewa, ya gudu daga kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China